Home Labarai Ku nemo wa kanku hanyoyi samun kuɗi – gwamnatin tarayya ga asibitoci

Ku nemo wa kanku hanyoyi samun kuɗi – gwamnatin tarayya ga asibitoci

147
0

Ministan lafiya na Nijeriya Dr Osagie Ehanire ya yi kira ga asibitocin ƙasar, su nemar wa kan su ƙarin hanyoyin samun kuɗaɗe don tabbatar da ingataccen aikin samar da lafiya.

Ehanire ya bada wannan shawara ne a lokacin da yake duba wasu kaya a babban asibitin ƙasa da ke Abuja.

Ya ce idan asibitocin suka yi haɗin guiwa da ɓangarori masu zaman kan su, za su ƙara samun kuɗi, sannan kuma dole su san ta yadda za su riƙa kashe kuɗinsu, domin a cewarsa, gwamnati ita kaɗai ba za ta iya biya masu buƙatunsu ba.

A nasa jawabin shugaban asibitin Dr Jaf Momoh ya ce akwai likitocin Nijeriya da dama da suke barin ƙasar saboda abun duniya, kuma har yanzu ba a maye gurbinsu da wasu ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply