Home Labarai Ku tsige tare da daure duk basaraken da aka samu da hannu...

Ku tsige tare da daure duk basaraken da aka samu da hannu a ta’addanci-Sultan

87
0

Abdullahi Garba Jani

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya yi kira ga gwamnonin kasar nan da su tsige tare da daure duk wani basaraken da aka samu yana taimakon masu aikata ta’addanci a gundumarsa.

Sarkin musulmin ya bayyana cewa abin takaici ne zargin tsoma hannun wasu masu rike da saraitun gargajiya a cikin aikata ta’addanci.

Alh Sa’ad Abubakar ya yi wannan kiran ne a wani taron inganta tsaro da majalisar masarautarsa hadin guiwa da kungiyar ‘yan jarida reshen Sokoto suka shirya.

Ya ce za su ci gaba da taimako da goyon bayan duk wani gwamna kan wannan batun domin ya samu damar daukar mataki kan duk wani basaraken da aka samu da hannu a aikata wannan bahallatsa.

Alh Sa’ad Abubakar ya ce ya zama wajibi a yi wa matsalar kofar-raggo ta yadda mutane za su rika barci idanunsu a rufe.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply