Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci hukumar zaɓen Nijeriya INEC ta yi amfani da zaɓen gwamnan jihar Osun da za a gudanar ranar Asabar, 15 ga Agusta 2026, wajen nuna irin shirin da ta yi na tunkarar babban zaɓen 2027.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Tinubu ya kuma umurci jami’an tsaro su tabbatar an gudanar da zaɓen cikin lumana, gaskiya da adalci, tare da kare jami’an zaɓe da masu kaɗa ƙuri’a daga duk wani nau’in barazana ko tsoratarwa.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya yi kira ga al’ummar Osun su fito su gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali.
Shugaban ya ce dole ne INEC ta tabbatar zaɓen ya kasance cikin tsari, gaskiya da adalci, yana mai cewa sakamakon zaɓen ya kamata ya nuna ainihin ra’ayin al’ummar jihar.
Tinubu ya ce zaɓen Osun shi ne zaɓen gwamna na ƙarshe da za a gudanar kafin babban zaɓen 2027, don haka INEC ya kamata ta yi amfani da shi a matsayin gwaji domin nuna wa ’yan Nijeriya cewa ta shirya tsaf domin babban zaɓen.
Ya kuma bayyana cewa ya umurci sufeto-janar na ’yan sanda da sauran shugabannin hukumomin tsaro da za su shiga aikin tabbatar da tsaron zaɓen su samar da cikakken tsaro a rumfunan zaɓe.
Shugaban ya gargadi masu neman tada rikici da kada su yi ƙoƙarin kawo cikas ga zaɓen domin ba za a bari a tsoratar da masu zaɓe ko jami’an zaɓe ba.
A zaɓen na Asabar, ’yan takara 15 ne za su fafata, ciki har da gwamnan jihar mai ci, Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord, ɗan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji, da ɗan takarar jam’iyyar ADC, Najeem Salaam.
Tinubu ya ƙara kira ga masu kaɗa ƙuri’a da su fito kwai da kwarkwata domin zaɓar ɗan takarar da suke so, tare da basu kwarin gwiwa cewa an ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da zaɓe cikin lumana da tsaro.
