Home Addini Ku yi kiwon zakara domin samun falala – Dr Sani Rijiyar Lemo

Ku yi kiwon zakara domin samun falala – Dr Sani Rijiyar Lemo

133
0

Babban Malamin addinin musuluncin nan, Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar lemo ya ja hankalin al’ummar musulmi tare da kwadaitar da su ribar a  kiwon Zakara.

 

Babban Malamin ya yi wannan jan hankali ne a jiya Laraba lokacin da yake gabatar da karatun Littafin “Alwabilussayyib” Littafin da yake bayani a kan addu’oi da Zikirai,

A darasin sa na (148) wanda ya saba gabatarwa a dukkan ranakun Laraba bayan Sallar Magriba a Masallacin Cibiyar Imamul Bukhari dake Rijiyar Zaki cikin Birnin Kano.

A lokacin da Babban Malamin yake tsaka da bayani a kan Hadisin Annabi (S.A.W) wanda Abu Huraira ya rawaito, Al-imamul Bukhari da Muslim suka fitar dashi a cikin ingantattun littafansu, Hadisin da Annabi mai tsira da amincin Allah yake cewa:

“Idan kun ji cara (Kukan) Zakara to ku roki Allah daga Falalar sa, domin ya ga Mala’ika ne.”

A karkashin haka sai Malamin ya ja hankalin al’ummar musulmi, ya kuma kwadaitar dasu a kan yin kiwon Zakaru, domin dai idan Zakara ya yi cara ya ga Mala’ikun Rahama ne.

Kuma duk Mutumin da yayi addu’a a lokacin ana masa fatan amsawa daga Allah, saboda Mala’iku za su taya shi da cewa: “Amin.”

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply