Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC a zaben 2027, Peter Obi, ya bukaci ‘yan Nijeriya su rika yin tambayoyi masu tsauri kan halin da kasar ke ciki da kuma yadda za a magance matsalolinta.
Obi ya yi wannan kiran ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a ranar Juma’a a Onitsha, jihar Anambra, inda ya sanar da fara yakin neman zabe gabanin zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki da aka shirya gudanarwa a ranar 16 ga Janairu.
Ya ce Nijeriya na fuskantar manyan kalubale da dama, wasu daga cikinsu kuwa suna barazana ga wanzuwar kasa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Obi ya ce yana ganin kansa a matsayin wanda ya dace ya nemi kuri’ar ’yan Nijeriya domin magance matsalolin kasar.
Ya ce kwarewarsa a harkar kamfanoni masu zaman kansu, karatunsa a manyan cibiyoyin ilimi kan manufofin gwamnati da harkokin kasuwanci, da kuma kwarewar da ya samu a matsayin gwamnan Anambra sun sanya shi cikin wadanda suka fi dacewa da aikin.
Obi ya ce abokin takararsa, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya zo da wata kwarewa ta shugabanci wadda ta dace da tasa, musamman wajen mayar da hankali kan ilimi, koyar da sana’o’i, tallafin karatu, ababen more rayuwa da bunkasa kwarewar jama’a a lokacin da yake Gwamnan Kano.
Ya ce jarin da gwamnatin Kwankwaso ta yi a fannin ilimi da koyar da sana’o’i ya nuna fahimtar cewa mutane su ne babbar dukiya ta dogon lokaci ga kowace jiha.
Obi ya yi alkawarin cewa idan aka zabe su, gwamnatin Obi-Kwankwaso za ta kara yawan amfanin gona ta hanyar kare manoma da al’ummomin da ke aikin noma, fadada ban ruwa, inganta hanyoyin karkara da wuraren adana amfanin gona, tare da hada manoma da hanyoyin samun kudade da kasuwanni.
Ya kuma ce za su karfafa masana’antu da sarrafa amfanin gona domin Nijeriya ta kara fitar da kayayyakin da aka kammala sarrafa su zuwa kasashen waje, tare da samun karin darajar tattalin arziki daga albarkatun kasar.
Dangane da tsaro kuwa, Obi ya ce gwamnatinsa za ta inganta tattara bayanan sirri da hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, tare da karfafa aikin ’yansanda da kula da iyakokin kasa da kuma amfani da fasahar zamani yadda ya kamata.
Ya kuma yi alkawarin tallafa wa tsarin tsaron al’umma da doka ta amince da shi, domin gano barazanar tsaro tun da wuri da kuma ba da damar daukar matakin da ya dace cikin gaggawa.
