Ministar kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmad ta ce kudaden shigar da Nijeriya ke samu ya ragu da kaso 65%.
Zainab Ahmad ta ce wannan dalilin ns ya sa shugaban kasa Muhammad Buhari ya ce ba zai sake biyan tallafin man fetur ba.
A zantawarta da gidan talabijin na NTA a shirin “Good Morning Nigeria” Zainab Ahmad ta ce idan aka ci gaba da biyan tallafin man, to kuwa zai yi karanci don gwamnati ba za ta iya biyan ‘yan kasuwar man ba.
