Home Labarai Kudirin bada rigar kariya ga ‘yan majalisar Nijeriya ya raba kan ‘yan...

Kudirin bada rigar kariya ga ‘yan majalisar Nijeriya ya raba kan ‘yan majalisar wakilai

63
0

Kudirin dokar bada kariya ga shugaannin majalisun dokokin jihohi da na tarayya ya tsallake zuwa karatu na biyu a majalisar wakilai ta tarayya.

Kudirin dai wanda ke neman yin gyara ga sashe na 308 na kundin tsarin mulkin Nijeriya da zai fadada rigar kariya har zuwa ga shugabannin majalisar, wanda Olusegun Odebunmi ya dauki nauyi, ya tsallake karatu na farko ne da kyar, ganin yadda kudirin ya raba kan ‘yan majalisar.

Tun kafin gabatar da kudirin don tafka muhawara a kan sa da, Kakakin majalisar Femi Gbajabiamila ya nuna kin amincewar sa ga kudirin da ya nuna cewa babu wata fa’ida da zai iya kawowa.

Ya nuna cewa zai goyi bayan kudirin ne kadai, idan zai fara aiki daga shekarar 2023, lokacin da gwamnati mai ci ta kare wa’adin ta.

Daga bisani ‘yan majalisar sun bukaci a tura kudirin ga ‘yan Nijeriya ta hanyar sauraron ra’ayoyin jama’a domin su amince, ko kin amincewa da shi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply