Ƙungiyar ɗaliban Nijeriya (NANS) ta yi watsi da kiraye-kirayen da wasu ‘yan siyasa ke yi na a dawo da tallafin man fetur, tana mai cewa hakan zai sake jefa ƙasar cikin matsalar tattalin arziki.
Jaridar Punch ta ruwaito shugaban NANS na ƙasa, Babatunde Akinteye, ya bayyana haka a ranar Talata a Akure, babban birnin Jihar Ondo, yayin wani taron matasa mai taken “Unlocking Ondo State Students’ Potentials for Economic Growth.”
Akinteye ya ce Nijeriya ta shafe kusan shekaru 40 tana gudanar da tsarin tallafin man fetur, amma gwamnatoci da masana tattalin arziki sun dade suna bayyana tsarin a matsayin wanda ba ya daɗewa saboda asarar da yake jawowa gwamnati.
Ya ce maimakon a nemi dawo da tallafin, ya kamata ‘yan Nijeriya su mayar da hankali wajen tabbatar da cewa ana amfani da kuɗaɗen da ake samu sakamakon cire tallafin cikin gaskiya da rikon amana, tare da karkatar da su zuwa ayyukan da za su amfani al’umma.
Ya ƙara da cewa a lokacin da ake biyan tallafin, har yanzu ‘yan Nijeriya na fuskantar ƙarancin man fetur da dogayen layuka, duk da makudan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa.
Shugaban NANS ya kuma ce farashin man fetur ya fara raguwa kafin barkewar rikicin Iran da Amurka, yana mai cewa rikicin ya taimaka wajen haifar da sabon tashin farashin.
A cewarsa, dawo da tallafin zai ɗora wa gwamnatin tarayya wani nauyi mai tsanani na kuɗi, inda ya tambayi inda za a samo ɗimbin kuɗaɗen da za a riƙa amfani da su wajen biyan tallafin.
Akinteye ya buƙaci duk wani ɗan siyasar da ke son jagorantar Najeriya ya gabatar da sahihin shiri kan yadda za a yi amfani da kuɗaɗen da ake samu daga cire tallafin wajen inganta rayuwar jama’a, maimakon yin alkawarin dawo da tsarin.
Ya kuma bayyana asusun ba da lamunin karatu na Nijeriya (NELFUND) a matsayin ɗaya daga cikin shirye-shiryen da suka taimaka wa ɗalibai tun bayan cire tallafin man fetur.
Akinteye ya ce dawo da tallafin da wasu ‘yan siyasa ke kira a kai ya fi kama da maganar siyasa, ba wai wata manufa ce mai ɗorewa ta tattalin arziki ba.
