Home Kasashen Ketare Kungiyar AU ta yi tir da kisan farar hula a Ethiopia

Kungiyar AU ta yi tir da kisan farar hula a Ethiopia

96
0

Kungiyar hada kan nahiyar afrika AU ta yi tir da kisan fararen hula a kasar Ethiopia, inda kungiyar ta yi kiran da gaggauta hukunta wadanda suka yi wannan aika-aikar.

Shugaban kungiyar Moussa Faki Mahamat a cikin wata takarda daga ofishinsa, ta ce Faki ya yi takaicin wannan kisa.

Kungiyar kare hakkin dan’Adam ta sanar da cewa an yi wa wasu fararen hula 32 kisan gilla a lardin Oromia na kasar Ethiopia.

Karin biyu daga cikin wadanda suka samu raunuka daga baya su ma sun ce ga garinku nan, da jimillar ta zamo 34.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply