Home Labarai Kungiyar mata ta dauki nauyin yi wa yara kaciya a Sokoto

Kungiyar mata ta dauki nauyin yi wa yara kaciya a Sokoto

56
0

Kungiyar mata ta FOMWAN a Nijeriya reshen jihar Sakkwato ta soma daukar nauyin yi wa yara 100 kaciya a kokarinta na saukaka wa iyaye masu dan karfi.

A Wata sanarwa da shugabar kungiyar Malama Zainab Ahmad Binji ta fitar, tace aikin kaciyar dai ya zakulo yaran ne a galibin gidajen marassa galihu, inda za su kula da maganin su har sai sun warke tare da kula da dawainiyar cin su da shan su.

Wannan aikin dai ana ganin ba karamin taimako bane musamman ga marassa galihu din.

Tuni dai iyayen yara da aka zakulo za a yi wa ‘yayan su Kachiyar keta bayyana jin dadi ga kungiyar matan ta FOMWAN.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply