Home Kasashen Ketare Kungiyar “OPEC” ta cika shekaru sittin da kafuwa

Kungiyar “OPEC” ta cika shekaru sittin da kafuwa

86
0

Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC ta bayyana cewa kasuwar sinadarin “Hydrocarbons” na dada samun tagomashi a kasuwar duniya, hakan ya sa kungiyar za ta ci gaba da kasuwancinsa har nan da shekaru sittin masu zuwa.

Muhammad Sunusi Barkindo shi ne shugaban kungiyar, ya bayyana haka a wajen bikin cikar kungiyar shekaru sittin da kafuwa.

Barkindo ya ce ko shakka babu kungiyar ta yi rawar gani tun daga farkon kafa ta har zuwa yanzu, ya ce har yanzu manufar kungiyar na nan kamar da.

Hakan ta sanya kungiyar ke ci gaba da ayyukan jin kai da suka shafi kula da muhalli, samar da makamashi da ma kawar da talauci a fadin kasashen.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply