Home Labarai ‘kurme’ a rafin kauye ya halaka wani yaro

‘kurme’ a rafin kauye ya halaka wani yaro

70
0

Abdullahi Garba Jani

Hukumar ‘yan kwana-kwana a jihar Kano ta tabbatar da cewa wani tafki a Sharada Kwanar Maijego ya cinye wani yaro mai shekaru 12 Isma’ila Safiyanu a lokacin da yake wanka ciki.

Mai magana da yawun hukumar kwana-kwanan Alhaji Sa’idu Muhammad wanda ya tabbatar da faruwar lamarin yace abin ya auku a daidai lokacin da yaron ya je wanka cikin tafkin.

Wasu yara na kurme a rafin kauye

Yace wani Malam Jamilu Yahaya ne ya kira hukumar ya ke ce mata an ga gawar yaron na yawo bisa ruwa a cikin tafkin.

Hukumomi na yawan jan kunnen iyaye kan su rika lura da ‘ya’yansu musamman a wannan zamani na damina da ake ciki.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply