Home Kasashen Ketare Kuru’un Electoral College na Biden sun kai 306 a ranar Jumma’a

Kuru’un Electoral College na Biden sun kai 306 a ranar Jumma’a

157
0

Gidan Talabijin na CNN ya bayar da labarin cewa Joe Biden shi ne dan takarar jam’iyyar Democrat a Amurka da ya lashe zabe a jihar Georgia a cikin shekaru 28. CNN ta ce kawo yammacin Jumma’ar nan kuru’u 16 na wakilan masu zabe (Electoral College) da Biden ya samu a jihar Georgia sun sa yanzu yana da kuru’u 306, adadin kuru’un da Shugaba Donald Trump ya samu a zaben 2016.

VOAHausa  kuma ya ruwaito cewa nasarar da Biden din ya yi a Georgia ita ce ta farko ga jam’iyyar Democrats tun bayan da Bill Clinton ya yi shekarar a 1992, tun daga wancan lokaci jam’iyyar Republican ce ke lashewa sai a wannan karon da mutanen jihar suka zabi Joe Biden.

Ana kallon wannan kuru’u sun ba Biden damar samun gagarumar nasara domin shi Donald Trump CNN ta yi hasashen kuru’un wakilan masu zabe 232 ya samu idan har an kammala tattara sakamakon zaben.

Wannan dai ya kara  tabbatar da nasarar Zababben Shugaban na Amurka Joe Biden. Sai dai har kawo yanzu Shugaba Donald Trump ya gaza amsa shan kaye, yana ci gaba da cewa an yi masa magudi a zaben na 3 ga watan Nuwamba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply