Home Coronavirus Kusan rabin masu coronavirus na Afirka sun warke “Sarai”

Kusan rabin masu coronavirus na Afirka sun warke “Sarai”

272
0

 

Kusan rabin adadin mutanen da ya kamu da coronavirus a kasashen nahiyar Afirka ya warke. Kawo safiyar Jumma’ar mutane 195,729 ne suka warke daga a cikin mutum 414,011 da cutar ta corona ta kama a Afirka, acewar hukumar CDC mai kula da takaita bazuwar cututtuka a Afirka.

Kafin yanzu Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum biliyan daya za su iya kamuwa da cutar a Afirka. Kwalejin Imperial College ta Landan kuma a hasashenta mutum 300,000 corona za ta hallaka a Afirka. To amma bayanan da suka fito a wannan Jumma’ar sun nuna cewa Afirka ba ta kama hanyar shiga irin wannan kunci ba, domin yanzu gabadaya masu corona na Afirkan ba su wuce kaso 5 cikin 100 na masu cutar a duniya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply