Kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu
Bamalli Poly Zaria ta samu kudade da suka kai Naira milyan 7 daga gwamnatin jihar domin saya wa dalibai kayayyakin kariya daga cutar corona.
shugaban kwalejin Dr Muhammad Kabiru Abdullahi ya sanar da haka a Zariya ya yin da ya ke ganawa da manema labarai.
Dakta Muhammad ya ce za su yi amfani da wadannan kudade ne wajen saya wa dalibai takunkumin rufe hanci da baki, da nau’ikan na’urar gwada zafin jiki, sinadarin wanke hannu na sanitizer da dai sauransu.
