Daga Abdullahi Garba Jani
Kulob din Inter Milan na kasar Italiya ya sayi danwasan Manchester United Romelu Lukaku kan kudi dala milyan 89.61.
A wata kafar watsa Labarai ta kasar Italiya ta ce Lukaku, dan wasan gaban kasar Belgium ya koma Inter Milan ne bayan da aka kammala ciniki tsakani.
Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa an ga Romelu Lukaku a hoton bidiyo a shafin Twitter na kulob din Inter Milan ya na cewa kowa zai iya zuwa ya murza Leda a kulob din.

Lukaku dan shekaru 26, ya buga wasanni 252 ya ci kwallaye 113 sannan ya taimaka aka zura kwallaye 35 a ya yin zamansa a kulob din Manchester United.
