Home Labarai Kwamishinonin ‘yansanda 9 sun samu mukamin AIG a Nijeriya

Kwamishinonin ‘yansanda 9 sun samu mukamin AIG a Nijeriya

49
0

Hukumar kula da ayyukan ‘yansanda ta Nijeriya ta yi karin girma ga kwamishinonin ‘yansanda 9 zuwa mukamin mataimakin babban Sufeton ‘yansanda na kasa AIGs.

Kazalika, hukumar ta yi karin girma ga mataimakan kwamishinan ‘yansanda DCPs 9 zuwa mukamin kwamishina CPs.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda daga mai magana da yawun hukumar Ikechukwu Ani, mai taken “hukumar kula da ayyukan ‘yansanda ta yi karin girma ga ‘yansanda 20,356, CPs zuwa AIG 9, DCPs zuwa CPs 9.

Sabbin wadanda suka samu mukamin mataimakin babban Sufeton ‘yansanda su ne Aminu Pai, Dasuki Galadanci, Okon Ene, Abang John, Joseph Mukan, Aji Ali Janga, Mukaddas Garba, Habu Ahmadu da Imohimi Edgal.

Mataimakan kwamishinan ‘yansanda da suka samu karin girma zuwa kwamishinan ‘yansanda su ne, Abubakar Alhaji, Benjamin Okolo, Abdul Yari Shuyagu, Oyediran Oyeyemi, Sama’ila Dikko, Jimwan Dazong, Monday Kuryas, Hussaini Rabi’u, da Rabi’u Umar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply