Home Sabon Labari Kwana guda bayan sarkin Rano, wani basarake ya sake mutuwa a Arewa

Kwana guda bayan sarkin Rano, wani basarake ya sake mutuwa a Arewa

78
0

Allah ya yiwa sarkin Ƙaura Namoda da ke jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Ahmed Asha rasuwa, da safiyar yau Lahadi.

Ana sa ran ya rasu ne sanadiyyar kamuwa da Covid-19.

Kamar yadda sakataren yaɗa labarun kwamitin yaƙi da cutar Covid-19 a jihar, Alhaji Mustafa Jafaru Ƙaura ya faɗa, an keɓance sarkin ne a babban asibitin Yarima Bakura Specialist da ke Gusau, kwanaki uku da suka wuce.

Mustafa ya ce an aiki da jinin sa a Abuja domin yin gwaji, saidai kafin sakamakon ya dawo ne sarkin ya ce ga garin ku nan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply