Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Rufa’i Sani Hanga, ya ce ya raba gari da tsohon gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya Rabiu Musa Kwankwaso ne sakamakon abin da ya bayyana a matsayin kishi da kyashi kan kan ayyukan da yake gudanarwa da shirye-shiryen tallafa wa jama’a.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Hanga ya bayyana hakan ne a wata hira da tashar talabijin na yanar gizo Dan’uwa Rano TV, inda ya ce Kwankwaso bai jin daɗin yadda jama’a ke yabonsa da nuna godiya kan ayyukansa, lamarin da ya ce ya taimaka wajen ƙara dagula alaƙar da ke tsakaninsu.
Hanga ya ce rashin jituwar ta ƙara bayyana ne bayan da ya shirya wani babban shirin tallafa wa al’ummar mazabarsa, inda aka raba motoci, buhunan shinkafa, taki, injinan niƙa, dabbobi da sauran kayayyaki ga waɗanda suka amfana.
A cewarsa, kayan tallafin sun yi yawa har aka shafe kusan kwana ɗaya da rabi ana jigilar su zuwa wurin da aka gudanar da taron.
Hanga ya ce lokacin da Kwankwaso ya isa wurin ya ga irin yawan kayan tallafin, sai ya nuna rashin jin daɗi, daga bisani ya nemi a dakata domin a yi sallah sannan ya bar wurin ba tare da ya dawo ba.
Sanatan ya ce daga baya Kwankwaso ya tunkare shi kan shirin, inda ya nuna damuwa kan yadda jama’a ke yabonsa saboda irin ayyukan da yake gudanarwa a matsayin Sanatan Kano ta Tsakiya.
Hanga ya ce ya nemi afuwar Kwankwaso tare da yin ƙoƙarin warware rashin fahimtar da ta samu tsakaninsu.
Ya kuma ce lamarin ya taimaka wajen fahimtar cewa alaƙar mutuntawa da ke tsakaninsu ta fara sauyawa, lamarin da daga baya ya haifar da rarrabuwar siyasarsu.
Hanga ya ƙara da cewa rashin jituwar da ta shiga tsakaninsa da Kwankwaso ta shafi makomar siyasarsa, musamman batun samun damar sake tsayawa takara a ƙarƙashin tsarin siyasar Kwankwassiya.
Sanatan ya ce, a ganinsa, rashin jin daɗin Kwankwaso kan ayyukansa da shirye-shiryen tallafa wa jama’a na daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen lalacewar dangantakarsu.
