Home Labarai Kwankwaso ya tarbi ɗalibai 370 da ya tura karatu ƙasashen waje

Kwankwaso ya tarbi ɗalibai 370 da ya tura karatu ƙasashen waje

30
0

Dalibai 370 ‘yan asalin jihar Kano da tsohon gwamnan kano Dr Rabiu Kwankwaso ya dauki nauyin karatun su na digiri sun dawo gida Nijeriya bayan kammala karatu a jami’o’i daban-daban a kasashen India, Dubai da kuma Sudan.

Majiyar Dcl Hausa ta ce tun watan Satumbar shekarar 2019 ne rukunin farko na daliban suka bar gida Nijeriya zuwa kasashen domin karin karatu.

Da ya ke tarbar daliban, Kwankwaso ya nuna matukar farin cikinsa, yana mai cewa yana farin cikin karbar daliban a gida cikin koshin lafiya.

“Wannan rana ce da za a tuna, rana ce mai matukar tarihi yayin da burinmu ya cika. ”inji shi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply