Home Labarai Kwanton Bauna: ‘Yan Ta’adda sun kashe sojojin Nijeriya 70

Kwanton Bauna: ‘Yan Ta’adda sun kashe sojojin Nijeriya 70

70
0

Kimanin sojojin Nijeriya 70 aka kashe a wani harin kwanton bauna da ‘yan ta’adda suka kai kan sojojin a jihar Borno, kamar yadda wata majiya ta nuna a yau Talata.

Wasu jami’an sojoji da suka boye sunayen su, sun shaidawa kamfanin dillanci labarai na AFP cewa, ‘yan ta’addar sun bude wuta kan wata babbar motar kwasar sojoji da fito daga kusa da kauyen Gorgi na jihar Borno a ranar Litinin.

Jami’an sun ce an raunata sjoji da dama, yayin da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da wasu.

Wani mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriyar, ya shaidawa AFP cewa ba zai samu damar yin magana kan harin ba.

Wani daga cikin jami’an gwamnati ya ce tawagar sojojin dai ta bar birnin Maiduguri ne zuwa kaddamar da wani hari a matattarar ‘yan ta’addan da ke da alaka da IS kafin a kai masu harin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply