Abdullahi Garba Jani/NIB
Magidanta a ƙananan hukumomin Birnin Kebbi, Jega da Danko-Wasagu da ke jihar Kebbin Nijeriya sun fara wani yinƙuri na dashen itatuwa don yaƙi da kwararowar hamada da sauyin yanayi a yankunan su.

Al’ummomim sun karɓi itatuwan dashe 268,000 daga cikin 360,000 da aka ƙiyasta suna buƙata domin dasawa, da manufar yaƙi da ƙalubalen gurɓacewar muhalli.
Itatuwan dashen da aka ba su sun hada da; lemu, zogale, mangwaro da sauransu.

Masana dai sun ce yawan sare itatuwa na haddasa ambaliyar ruwa, zaizayar kasa, kwararowar hamada da sauyin yanayi.
Yankin Arewa maso yammacin Nijeriya, wanda jihar Kebbi ke ciki, na ɗaya daga cikin yankunan da ke fama da wannan matsala a yammacin Nahiyar Afirika.
