Abdullahi Garba Jani
Ma’aikatar kula da muhalli ta Nijeriya ta ce kwararowar hamada ta mamaye kusan kaso 35% na yawan kasar hade da ci gaba da barazana ga sauran wurare.
Ministan muhalli na Nijeriya Dr Mahmood Muhammad ya fadi haka a Nangere jihar Yobe. Mahmood ya ce muhallan mutane sama da milyan 40 a jihohi kusan 11 ne ke da barazanar kwararowar hamada da zaizayar kasa.

Sai ministan ya bukaci masu ruwa da tsaki da su hadu don ganin an yi wa tufkar hanci.
A nasa bangare, gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni yace gwamnatinsa na aiki tukuru don ganin an shawo kan matsalar a duk wuraren da ke fuskantar wannan matsala.
