Home Farashin Kayan Abinci “Kwastam ke sa abinci na tsada a Jibiya”

“Kwastam ke sa abinci na tsada a Jibiya”

425
0

Al’ummar ƙaramar hukumar Jibia a jihar Katsina, sun bayyana rashin jin daɗinsu akan halin da suke zargin jami’an hukumar hana fasa ƙwabri ta ƙasa kwastan ta sanya su na sanya kayan abinci tsada a yankin.

Shugaban Ƙungiyar Matasa masu rajin ci gaban ƙaramar hukumar Nasiru Almustapha Danye ne ya sanar da hakan a wani taron Manema labarai a Katsina.

Nasiru Almustapha ya ce jami’an hukumar kwastam suna tsananta matakai ga duk wanda ya ɗauko kaya daga Katsina ko wani yanki na ƙasar nan zuwa Jibia duk kuwa da cewa babu haramci a kasuwancin kayan, irinsu masara, gero, Siminti, fulawa da sauransu.

Ya ce farashin ire-iren waɗannan kaya ya yi tashin-gwauron-zabi a ƙaramar hukumar Jibia sanadiyyar harajin da jami’an tsaro suke amsa kafin su isa garin.

Sai dai a nashi ɓangaren, babban jami’in hukumar ta kwastan a Katsina Abdullahi Kirawa ya ce hukumar ba ta haramta wa kowa kasuwanci ba muddin bai saɓa dokar ƙasa ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply