Home Labarai Kwastan sun kama buhunan shinkafa 3,111 da jarkokin man girki 1,138 ...

Kwastan sun kama buhunan shinkafa 3,111 da jarkokin man girki 1,138 a arewa maso yamma

80
0

Hukumar kwastan ta ce ta kama buhunan shinkafar waje 3,111 cikin watanni uku a arewa maso yammacin Nijeriya.

Kazalika, hukumar karkashin shiri na musamman na sa ido kan iyakokin kasar nan mai lakabin “Boarder Drill Operation” a shiyya ta 4 ta ce ta kuma yi nasarar kama dilolin atamfa 46 da na gwanjo 43.

Jami’in da ke kula da shirin shugaban kasa na sa ido kan iyakokin tudu na “Boarder Drill Operation” mai kula da shiyyar arewa maso yamma Aliyu Muhammad ya sanar da hakan a Katsina a lokacin da ya ke karin haske ga manema labarai kan irin nasarorin da suka samu a watanni uku.

Aliyu Muhammad ya ce jami’an rundunar sa idon ta “Boarder Drill” sun kuma kama daurin tabar wiwi 155 da motoci 9 da kuma jarkokin man girki 1,138.

Ya kara da cewa a cikin watannin Agusta, Satumba da Oktoba, rundunar ta kuma yi nasarar kama katan-katan na taliyar Spaghetti ta waje 831 da buhunan sukari 98.

Aliyu Muhammad ya ce rundunar ta yi jimillar kamen kaya 254 a cikin watanni ukun.

Ya yi kira ga al’umma da su rika taimakon jami’an su da bayanai sahihai domin ganin an bi doka da oda ta fuskar shige da ficen kayayyaki.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply