Home Labarai Kwastan sun kama buhunan shinkafa a Nijeriya

Kwastan sun kama buhunan shinkafa a Nijeriya

123
0

Hukumar hana fasa kwauri ta Nijeriya (Kwastam) ta ce ta kama akalla buhunna 1000 na shinkafa da aka shigo da ita a karamar hukumar Mbo ta jihar Akwa Ibom.

Mai kula da Kudu-maso-Kudu da Kudu-Maso-Gabas, na hukumar, Shehu Abubakar, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci jami’an hukumar da suka gudanar da wanna samame a yankin na Uyenhe na jihar.

Abubakar ya kuma bayyana cewa jami’ansu za su ci gaba da binciko wuraren ajiyar ‘yan fasa-kwauri a yankin matukar suka ki daina irin wannan kasuwanci da gwamnati ta haramta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply