Tawagar hadin guiwa ta hukumar kwastan shiyya ta 4 a arewa maso yammacin Nijeriya da ke Katsina tace ta yi nasarar kama buhunan shinkafar bature 1,312 a cikin watan Janairun 2021 a shiyyar.
A taron manema labarai a Katsina, shugaban rundunar ta musamman Aliyu Alhaji Muhammad, yace tawagar ta kuma yi nasarar kama dunkulen tabar wiwi mai nauyin kilo 990 duk a cikin watan Janairun.
Yace kwastan din sun kuma yi nasarar kamen litar man fetur 864 da dilolin gwanjo 78 masu nauyin kilo 200 kowane a cikin wannan kankanin lokaci.
Aliyu Muhammad yace a cikin kame 56 da suka samu nasarar yi ne suka kama yawan wadannan kayan. Yace jimillar “dutin” kayan ya kama Naira milyan 152,866,000.
