Home Labarai Kwastan ta kama kaya na miliyoyin Naira a Kebbi

Kwastan ta kama kaya na miliyoyin Naira a Kebbi

24
0

Hukumar hana fasa kwabri ta Nijeriya ta ce ta kwace kaya 227 a shekarar da ta gabata.

Kwantarolan hukumar Hafiz Kalla ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa ‘yanjarida bayani kan nasarorin da hukumar ta samu a shekarar da ta gabata.

Ya ce an kwace kayan ne a kan iyakokin Kamba, Kangiwa da kuma Yauri, yana mai cewa darajar kayan ta haura Naira Miliyan dari 320 da dubu dari 701.

Ya kara da cewa hukumar ta kwace tare da yin gwanjon lita dubu dari da 25 ta man fetur da man dizel, da sauran wasu kayayyaki, kan kudi Naira miliyan 35, kuma an tura kudin ne a asusun gwamnatin tarayya.

Hafiz Kalla ya ce daga cikin kayan da aka amshen, akwai katan 333 na tabar wiwi, buhu dubu 3999 na takin zamani, buhu dubu biyu da 21 na shinkafar waje da dai sauransu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply