Hukumar hana fasa kwauri ta Nijeriya “kwastan” a Onne Port Harcourt jihar Rivers ta ce ta tattara kudaden shiga Naira bilyan 13.11 a watan Satumba.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda daga mai magana da yawun hukumar a birni Fatakwal Ifeoma Ojekwu.
Takardar ta ambato shugaban hukumar a shiyyar Awwal Muhammad na cewa shekaru 37 rabon da a tattara irin wadannan kudi a irin wannan lokaci.
Awwal Mohammad ya ce an samu nasarar tattara kudaden ne ta hanyar tabbatar da an biya kudaden haraji tare da hana ‘yan sumogal cin karensu ba babbaka.
