Home Kasashen Ketare Kyamar Baki: Afrika Ta Kudu za ta dauki mataki akan masu kai...

Kyamar Baki: Afrika Ta Kudu za ta dauki mataki akan masu kai hari

73
0

Hannatu Mani Abu

Gwamnatin kasar Afrika ta kudu ta ce ta kama mutane 90 da laifukan da suka jibinci nuna kyama ga baki da kwashe musu dukiyoyi.

A wata sanarwa da kafar sadarwar gwamnatin kasar ta fitar, ta bayyana cewa nuna rashin mutunci da rashin da’a a matsayin hanyar nuna bacin rai ba daidai ba ne.

Sai gwamnatin ta yi kira da a kwantar da hankali musamman a yankunan Gauteng da kwazulu Natal, biyo bayan kira da al’ummomin yankin suka yi akan matsaloli daban-daban.

Sanarwar ta ce bai kamata a balle wa mutane shaguna ba, tare da toshe hanyoyi, wanda yin hakan laifuka ne wadanda ke bukatar sa idon jami’an tsaro tare da yin hukuncin daya dace.

Gwamnatin kasar ta ce ba za ta bari a ci gaba da tafiya ba kan gado ba, inda ta nuna bukatar daukar matakin gaggawa daga ‘yan sandan kasar.

An dai kama mutane 70 sakamakon balle shaguna da wargaza kayan mutane bisa dalilin jin zafi da nuna kyamar baki.

Wannan barazana ga baki musamman ‘yan Nijeriya ne ya sa gwamnatin Nijeriya ta kira wani taron gaggawa da jakadan kasar Afrika Ta Kudu a Abuja don tattauna batutuwan da hanyar da za a yi wa tufkar hanci.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply