Home Labarai Kyamar Baki: Daruruwan ‘Yan Nijeriya sun bukaci a dawo da su gida

Kyamar Baki: Daruruwan ‘Yan Nijeriya sun bukaci a dawo da su gida

67
0

Nuruddeen Ishaq Banye/dkura

Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Afirka ta Kudu ya ce, yawan ƴan Nijeriya mazauna ƙasar da suka nuna sha’awar su ta dawowa gida Nijeriya ya haura 400.

Jakadan Nijeriya a birnin Johannesburg Godwin Adama ya bayyana haka a lokacin wata ganawa ta wayar tarho da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN a Abuja.

Adama ya ce kamfanin jiragen sama na Air Peace ne ya yi tayin maido da ƴan Nijeriya mazauna ƙasar da ke buƙatar dawowa gida kyauta, biyo bayan hare-haren nuna ƙyamar baƙi da ake kai masu, da kuma kasuwancin su.

A cewar Jakadan, za a fara jigilar ƴan Nijeriyar da ke son komawa gida a ranar Laraba mai zuwa.

Shima babban Jakadan Nijeriya a Afirka ta Kudu Kabiru Bala, ya ce ƴan Nijeriya sun bada haɗin kan da ake buƙata.

Shima a nasa ɓangaren shugaban ƙungiyar ƴan Nijeriya mazauna Afirka ta Kudu NICASA, Ben Okoli ya ce an gama dukkan shirye shirye na ɗauke ƴan Nijeriya daga ƙasar, kuma suna nan suna bakin ƙoƙarin su, na ganin an biya waɗanda aka yiwa ɓarna diyya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply