Home Labarai Labari a hoto: Shugaba Buhari na jagorantar taron majalisar tsaro

Labari a hoto: Shugaba Buhari na jagorantar taron majalisar tsaro

63
0

Yanzu haka shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar taron majalisar tsaron Nijeriya a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kundin tsarin mulkin kasa dai ya dora wa majalisar alhakin ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron al’umma.

Manyan jami’an gwamnati ne dai ke halartar taron wadanda suka hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, shugaban Ma’aikata na fadar shugaban Kasa Ibrahim Gambari da kuma mai ba shugaban kasa sharawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai murabus.

Sauran sun hada da manyan hafsohin tsaron kasar, da sufeton ‘yan sandan Nijeriya, da shugaban hukumar tsaron farin kaya da kuma shugaban leken asiri ta kasar da sauran ministoci da jami’an gwamnati.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply