Home Labarai Labarin bullar Covid-19 a majalisa karya ne, ya fi cin hanci muni...

Labarin bullar Covid-19 a majalisa karya ne, ya fi cin hanci muni – majalisar Dattawa

136
0

Majalisar Dattawan Nijeriya, ta karyata wani rahoto da wata kafar intanet ta yada cewa majalisar ta shiga fargaba, bayan an tabbatar ‘yan majalisa 50 sun kamu da cutar Covid-19.

Da yake maida martani, Shugaban kwamitin majalisar kan yada labarai Sanata Ajibola Basiru, ya bayyana labarin a matsayin labarin karya.

Rahoton dai, ya ce majalisar wakilai ta dage zamanta zuwa sati mai zuwa saboda an samu wasu ‘yan majalisar sama da 50 da suka kamu da cutar.

Jaridar, ta kuma an bato wani dan majalisa da bata bayyana sunansa ba, da yake shaidawa ‘yan jarida cewa kimanin ‘yan majalisa 50 suka kamu da cutar, kuma wasu daga cikin su na cikin mawuyacin hali.

Saidai kuma a wani sakon twitter, mai magana da yawun majalisar, ya dage da cewa labarin karya ne, wanda ya fi cin hanci muni.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply