Home Labarai Laccara ya fadi ya mutu yana tsaka da koyar da dalibai

Laccara ya fadi ya mutu yana tsaka da koyar da dalibai

39
0

Shugabannin Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Alvan Ikoku, AIFCE a garin Owerri, sun tabbatar da mutuwar wani babban malami a makarantar da yake tsangayar koyar da ilimin kasuwanci, mai suna Mista Echetama, wanda ya fadi ya mutu a yayin da yake tsaka da koyar da dalibai a cikin aji a ranar Talatar makon nan.

Mukaddashin jami’in hulda da jama’a na kwalejin, Joseph Okwulehi, ne ya tabbatar da mutuwar ga manema labarai a ofishinsa, ranar Laraba.

Joseph ya ce tuni shugaban kwalejin ya kira tarukan gaggawa dangane da batun mutuwar malamin.

A halin yanzu, an tilasta wa ɗaliban kwalejin su daina yin lacca sakamakon jita-jitar da ake yadawa na cewa mutuwar malamin na da alaƙa da COVID-19.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply