Home Lafiya Lafiya: Kungiyar Tarayyar Turai Ta Kawo Euro 300,000 Don Kyautata Lafiyar Kananan...

Lafiya: Kungiyar Tarayyar Turai Ta Kawo Euro 300,000 Don Kyautata Lafiyar Kananan Yara A Zamfara Da Sokoto

66
0

[cmsmasters_row data_width=”boxed” data_padding_left=”3″ data_padding_right=”3″ data_top_style=”default” data_bot_style=”default” data_color=”default” data_bg_position=”top center” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_size=”cover” data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_padding_top=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_shortcode_id=”am18gzz6″][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_bg_position=”top center” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_size=”cover” data_border_style=”default” data_animation_delay=”0″ data_shortcode_id=”7mdptwdsr”][cmsmasters_text shortcode_id=”hog7aabmd” animation_delay=”0″]

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta sanar da bayar da agajin kudi na Euro 300,000 kwatan-kwacin Naira Bilyan 120  domin dakile barazanar da kananan yara  280,000 ke fuskanta ta bangaren kiwon lafiya. Kungiyar ta EU ta ce ta yi haka ne don ta fahimci yaran  basu samun abinci mai gina jiki  a jihohin Zamfara da Sokoto da ke Arewa Maso yammacin Nijeriya.

 

Kamar yadda jaridar DailyTrust ta ruwaito Asusun yara na duniya UNICEF  ya bayyana cewar kimanin yara  280,000 yan kasa da shekaru 5 a jihohin Sokoto da Zamfaran ke fama da matsalar tamowa, hakan kuma na barazana ga rayuwar su. Asusun UNICEF ya kara da cewa ya yi amannar yaran na fuskantar karancin  rigakafi kan cututtuka masu kisa ga kananan yara.

 

Kwamishinan da ke kula da bayar da agaji a wuraren da ake rikici na hukumar EU Christos Stylianides ya ce agajin kudin da EU ta bayar zai taimaka wajen samar da abubuwa tare da lura da yaran da kuma samar da ci gaba ga bukatunsu na kiwon lafiya. Wannan yana da muhimmanci musamman ganin yadda wasu iyalai kan yi kaura don tsira da rayuwarsu a wadanann jihohi saboda rashin tsaro. Hukumar ta ce akasarin iyalan da ke barin gidajensu kan rasa tudun dafawa daga baya, a don haka akwai bukatar a kawo musu agaji.

 

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply