Home Labarai Lafiya: Yi wa Mata Kaciya Na Ci gaba da Dagula Musu lissafi...

Lafiya: Yi wa Mata Kaciya Na Ci gaba da Dagula Musu lissafi a Duniya-Masana

101
0

Abdullahi Garba Jani

Wata kwararriya a zamantakewar dan’Adam Mrs Abieyuwa Abeh, ta ce yi mata kaciya na jefa su cikin halin kunci, barazana ga lafiyarsu da wani irin yanayi na rashin nutsuwa.

Abeh ta fada wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya cewa matan, da ke cikin wannan hali na fuskantar matsalar tabin hankali yayin rayuwarsu da sauran kuntatawar rayuwa.

Yi wa mata kaciya dai na nufin yanka ko debe wani sashe na matuncinsu da sunan al’ada ko neman magani.

A kullum, kusan mata da ‘yan mata 6,000 ne ake yi wa kaciya. A duk duniya ma, an rigaya an yi wa mata da ‘yan mata sama da miliyan 200 kaciya, kamar yadda binciken hukumar lafiya ta WHO ya samo.

Ta ce akwai bukatar karfafa wa wadanda suka tsira daga shirin yi wa mata kaciya na su samu damar magana da kuma neman taimako.

Kwararriyar ta ce yawancin al’ummomi suna daukar al’adar yi wa mata kaciya a matsayin wata dadaddiyar al’adar da ba ta dace ba ta ci gaba tqna cewa wannan ba daidai bane saboda kaciyar ta mata wani mummunan aiki ne mai cutarwa ga ‘yan mata da mata tunda hakan yana lalata kusan rayuwarsu.

Mrs Abeh, ta shawarci mata da su ilimantar da ‘yan mata yadda za su iya zama mai ikon mallaka da ƙwarewa don yin zaɓin abubuwan da suke bukata

Ta yi kira ga gwamnati da ta himmatu wajen yin aiki tare da shugabannin addinai, ma’aikatan lafiya da ‘yan kasa don mayar da martani ga karbuwa ga al’adar wadda ke ci gaba da keta hakkin mata.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya tunaso cewa a ranar 2 ga Yuni, a Vancouver, Kanada, masu ruwa da tsaki a duk duniya, sun hallara don tattauna abin da ake buƙata don hanzarta kawo ƙarshen kaciyar mata nan da 2030.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply