Home Labarai Lafiya: za a yi wa yara 43,380 rigakafin cutar shan inna a...

Lafiya: za a yi wa yara 43,380 rigakafin cutar shan inna a jihar Jigawa.

84
0

SHARIFUDEEN IBRAHIM MUHAMMAD

Karamar hukumar Gumel a Jihar Jigawa ta fara shirin yi wa yara ‘yan ‘ka’sa da shekara biyar su 43,380 rigakafi cutar shan inna na watan Nuwamba.

Jami’in shirin rigakafin Alhaji Yusuf Tudun-Wada ya bayyana wa kamfanin dillacin labarai na Nijeriya a garin Gumel cewa, an fara aiwatar da shirin ne a ranar Asabar din nan, a karkare a ranar Litinin 5 ga watan Nuwambar nan.

Yace tuni karamar hukumar ta karbi sinadaran rigakafin da yawansu ya kai 41,340 daga gwamnatin Jihar kuma aka dauki ma’aikatan wucin-gadi domin gudanar da shirin.

Da yake na shi jawabi, Shugaban hukumar kula lafiya daga tushe na yankin, Alhaji Habu Magaji ya yi godiya ga Karamar hukumar bisa samar da katan 30 na kayan makulashe da a ka yi amfani da shi wajen jawo hankulan yara kanana.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply