Daga Hannatu Mani Abu
Dan wasan gaban kulob din Barcelona Louis Suarez ya samu rauni a kafarsa ta dama a lokacin wasan farko na gasar Laliga da suka kara da kulob din Atletico Bilbao.
Suarez ya samu rauni a mintuna na 37 da fara wasan, hakan ya jaza Barcelona ta rasa fitattun ”yan wasanta da suka samu raunuka, bayan da Messi ya samu rauni a farkon makon nan wajen atisaye.

Ya zuwa yanzu dai Barcelona ba ta fadi tsawon lokacin da Suarez zai kwashe yana jinya ba.
Atletico Bilbao ta zura kwallo daya a ragar Barcelona inda aka tashi ci 1-0.
Masu sharhi kan wasanni na ganin rashin wadannan mashahuran ”yan wasa ya jaza wa Barcelona wannan rashin nasara.
