A ranar Larabar makon nan ne lauyan marigayi Iyan Zazzau, Ustaz Yunus Usman SAN, ya garzaya kotu don janye karar da marigayin ya shigar na kalubalantar yadda aka ayyana Ambasada Ahmed Nuhu-Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19.
Hakan ya biyo bayan rasuwar Alhaji Bashar Aminu iyan Zazzau, da aka sanar da mutuwarsa a ranar Juma’a, 1 ga Janairu, 2021.
Yunus Usman ya shaida wa Daily Trust ta wayar tarho cewa ya kamata mu a cigaba da sauraren karar a Larabar makon nan. Sai dai abin takaici, a ranar 1 ga Janairu, 20201, mai shigar da kara, wanda ya ke karewa, Iyan Zazzau ya rasu.
