Home Labarai Lauyoyin Nijeriya sun maka Buhari kotu

Lauyoyin Nijeriya sun maka Buhari kotu

28
0

Kungiyar Lauyoyin Nijeriya ta fara daukar matakin shari’a kan matakin shugaban kasa Muhammadu Buhari na tsawaita wa’adin Muhammadu Adamu a matsayin Babban Sifetan ‘Yansandan Nijeriya.

Kungiyar na neman kotu ta fadi inda kundin tsarin mulki ya ba Buhari damar tsawaita wa’adin Adamu, bayan lokacin da doka ta dibar masa na shekara 35 a aikin gwamnati ya cika a ranar daya ga watan nan.

Ta ce akwai bukatar gaggawa na dawo da karfin doka a kasar a daidai lokacin da jami’an da ke tabbatar da dokar a cikin gwamnati suka kasa tsare hakkinta.

Kungiyar lauyoyin na kan matsayar cewa yanzu haka Adamu bai cikin jerin ‘yansandan Nijeriya, bayan cikarsa shekara 35 yana aiki, tana mai bayyana kara wa’adin nasa a matsayin saba kundin tsarin mulki.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply