Wani ƙwararren Lauya mai zaman kanshi mai suna Barista Olukoya Ogungbeje, ya gabatar da karar biyan diyyar Naira biliyan 10 a kotu, yana kalubalantar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Lauya Olukoya Ogungbeje ya kuma hada babban hafsan sojin kasa, Janar Tukur Buratai da wasu mutane a wannan shari’a a kan zargin harbe ‘yan zanga-zangar #EndSARS da aka yi a Lekki Jihar Legas.
Jaridar “Muryar ‘Yanci” ta ce lauyan ya na ikirarin jami’an tsaro sun bude wa bayin Allah masu zanga-zangar lumanar #EndSARS wuta a Lekki, a ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2020 bisa ga zalunci da cutarwa bisa ga umurnin Shugaban ƙasa da Shugaban dakarun Sojin ƙasa.
