Home Coronavirus Likitoci 20 sun mutu sakamakon corona a Abuja

Likitoci 20 sun mutu sakamakon corona a Abuja

122
0

Yanayin kula da majinyata ya karanta musamman a asibitocin birnin tarayya Abuja tun bayan komen cutar corona wanda ya shafi ma’aikatan lafiya ciki ha da likitoci.

Kungiyar likitoci reshen birnin tarayya a Juma’ar da ta gabata ta tabbatar da cewa sama da ‘yan kugiyarta 20 ne suka mutu daga cutar ta corona cikin sati daya.

Shugaban kungiyar reshen Abuja Enema Amodu ne ya bayyana hakan ya yin zantawa da manema labarai, yana mai cewa kwayar cutar na bukatar tashi tsaye dan ganin an magance yaduwarta.

DCL Hausa ta rawaito cewa, a asibitin Asokoro an tabbatar da cewa likitoci da yawa suna a killace sakamakon samunsu da aka yi dauke da wannan cuta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply