Home Labarai Likitoci sun janye yajin aiki a Zamfara

Likitoci sun janye yajin aiki a Zamfara

95
0

Kungiyar Likitoci reshen jihar Zamfara ta janye yajin aikin sati daya da ta shiga don nuna rashin amincewa kan hanasu alawus.

Shugaban kungiyar Mannir Bature ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, a garin Gusau.

Ya kuma bayyana cewa janye yajin aikin ya biyo bayan amincewa da maido masu alawus dinsu da gwmanatin Bello Matawalle ta yi bayan ganawa tsakanin gwamnatin da kuma wakilan kungiyar.

Shugaban ya yaba wa gwamna Matawalle kan kokarinsa na ganin an shawo kan matsalar, ya kuma godewa ƴan kungiyar tasu kan hadin kai da suke basu a ko da yaushe.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply