Home Coronavirus Likitocin 35 sun kamu da corona a Kwara

Likitocin 35 sun kamu da corona a Kwara

139
0

Kimanin likitoci talatin da biyar ne aka tabbatar sun kamu da cutar corona a jihar Kwara.

Shugaban kungiyar likitocin reshen jihar Dr Kolade Sholageru ne ya sanar da haka a ranar Litinin din da ta gabata a Ilorin babban birnin jihar.

Sai dai ya bayyana cewa har yanzu ba a kai ga samun wanda ya rasa ran sa ba daga cikin mambobin kungiyar.

A karshe ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi watsi da bayanan da suke yawo na cewa ana fakewa da corona wajen satar kudaden gwamnati.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply