Home Coronavirus Likitocin Nijeriya sun shiga yajin aiki

Likitocin Nijeriya sun shiga yajin aiki

67
0

Kungiyar Likitocin Nijeriya NARD ta tsunduma yaji aiki a ranar Litinin, bayan wa’adin gargadin kwana 14 da ta bayar ya cika.

Da yake magana da ‘yan jarida a ranar Litinin a Abuja, shugaban kungiyar Dr Aliyu Sokomba, ya ce yajin aikin zai ci gaba, ba tare da samun jami’an lafiyar da ke kula da masu cutar coranavirus a cibiyoyin killace masu cutar da dama da ke fadin kasar ba.

Kungiyar dai na nuna bacin rai, kan mawuyacin halin da asibitocin kasar ke ciki.

Kugiyar Likitocin dai, na kuma nuna damuwar ta ne, kan rashin samar da kayan kariya, ga ‘yan kungiyar da ke lura da masu cutar Covid-19.

Kungiyar ta kuma bada shawarar samar da kudin horas da likitocin a cikin kasafin kudin badi, tare da biyan dukkan kudaden ariyas da suke bin gwamnatocin tarayya da na jihohi tun bayan fara biyan mafi karancin albashi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply