Home Labarai Likitocin Nijeriya za su shiga yajin aiki

Likitocin Nijeriya za su shiga yajin aiki

102
0

Kungiyar Likitoci Nijeriya ta bada sanarwar tafiya yajin aiki daga ranar Litinin mai zuwa 15 ga watan Yuni.

Kugiyar ta ce yajin aikin zai hada har da likitocin da ke kula da masu cutar Covid-19 da sauran cutukun gaggawa.

Shugaban kungiyar Dr. Aliyu Sokomba ya ce dukkan likitocin kasar za su tafi yajin aikin ba tare da la’akari da halin da ake ciki ba.

Sokomba, ya ce daukar matakin ya zama wajibi, duba da kasawar gwamnati na cika alkawuran ta, musamman a bangaren albashi da kuma yanayin aiki.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply