Home Labarai Lokaci ya yi da gwamnatoci za su waiwayi kiwon lafiya – Ƙungiya

Lokaci ya yi da gwamnatoci za su waiwayi kiwon lafiya – Ƙungiya

27
0

Wata kungiar lafiya ta kasa ta yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai su suka harkar lafiya a matsayin na gaba-gaba cikin jerin tsare-tsarensu na ci gaba.

Kungiyar wadda ta kunshi kwararru 26 daga bangarori daban-daban na kiwon lafiya, ta yi wannan kiran ne a wajen taronta na shekara da ya gudana ranar Litinin, a Abuja.

Kwararrun sun ce yin hakan zai taimaka wajen samar da kudi ga sha’anin lafiya, da kuma ba kowa damar samun ingataccen kiwon lafiya da kuma samun kariya daga cutuka.

Shugaban kungiyar Honarabul Muhammad Usman, ya ce akwai bukatar fadada harkar lafiya ba wai daga gwamnatin tarayya ba kawai har ma a matakin jihohi.

Ya ce har kar lafiya ya dace ta zamo ta biyu daga cikin abubuwan da gwamnati za ta ba muhimmanci, musamman a gwamnatin tarayya, bayan matsalar tsaro, amma yanzu idan aka yi duba bangaren lafiyar shi ne mataki wajen na bakwai, wanda ya ce hakan baa bun da za a yarda da shi ba ne.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply