Home Labarai Ma’aikata za su riƙa zuwa aiki sau biyu a wata – Gwamnatin...

Ma’aikata za su riƙa zuwa aiki sau biyu a wata – Gwamnatin Lagos

51
0

Gwamanatin jihar Lagos ta yi bitar lokutan zuwa aiki ga ma’aikatanta a wani bangare na matakan dakile yaduwar cutar Covid-19 a tsakanin ma’aikatan.

Biyo bayan bitar matakan hana yaduwar cutar, shugaban ma’aikatan jihar Hakeem Muri-Okunola ya ce daga yanzu ma’akatan jihar za su rika zuwa aiki ne sau biyu kadai a wata.

Muri-Okunola wana ya koka da yadda ake yawan samun ma’aikatan da ke kamuwa da cutar, ya yi bayani cewa daukar wannan mataki ya zama wajibi duba da yadda gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Babajide Sanwo-Olu ta bada fifiko kan kare lafiyar ma’aikatanta.

A cikin wata takarda da aka aikewa ofisoshin akantocin jihar, ta roki jami’an su fitar da jadawalin zuwa aiki da zai dakile yaduwar cutar a hukumomi, ma’aikatu, sassa da bangarorin gwamnatin da suke wakilta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply