Home Coronavirus Ma’aikatan lafiya 75 sun kamu da corona a Katsina

Ma’aikatan lafiya 75 sun kamu da corona a Katsina

138
0

Ma’aikatan lafiya guda 75 sun kamu da cutar coronavm a jihar Katsina.

Kwamashinan yada labarai jihar AbdulKarim Yahaya Sirika ne ya sanar da haka ga manema labarai a Katsina.

Ya bayyana cewa ma’aikatan da suka kamu da wannan cuta na ci gaba da samun kulawa ta musamman a wurin da ake kula da masu corona a jihar.

Sai dai kwamashinan ya tabbatar da mutuwar wani likita da kuma wani ma’aikaci da ya ke aiki a dakin gwaje-gwajen cututtuka.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply