DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeLabaraiMa’aikatan lafiya a Katsina za su shiga yajin aikin gargadi

Ma’aikatan lafiya a Katsina za su shiga yajin aikin gargadi

Ƙungiyar ma’aikatan lafiya a jihar Katsina ta sanar da shirin fara yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki bakwai daga ranar Talata, 8 ga Satumba, 2026, saboda rashin warware wasu buƙatunsu da suka daɗe.

Jaridar Premium Times ta ruwaito shugaban ƙungiyar, Ibrahim Balange, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu tare da shugabanni da sakatarorin sauran ƙungiyoyin a ranar Talata a Katsina.

Sanarwar ta biyo bayan ƙarewar wa’adin kwanaki 21 da ƙungiyoyin suka bai wa gwamnatin jihar tun ranar 11 ga Agusta, domin ta magance buƙatunsu.

Balange ya ce wa’adin ya ƙare ba tare da gwamnati ta nuna gagarumin ƙuduri na magance matsalolin da ma’aikatan suka gabatar ba, duk da cewa ta amince cewa buƙatun nasu na da tushe.

Ya ce mambobin ƙungiyoyin sun yanke shawarar fara yajin aikin ne da tsakar dare na ranar 8 ga Satumba, inda za su ci gaba da shi na kwanaki bakwai a matsayin gargadi.

Ya ƙara da cewa idan gwamnatin Katsina ta gaza warware matsalolin bayan kwanaki bakwai, ma’aikatan za su shiga yajin aikin sai baba-ta-gani.

Balange ya kuma roƙi jama’a su fahimci matakin, tare da ɗora alhakin duk wata matsala da ka iya tasowa kan gwamnatin jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata